An saki wasu daga cikin daliban Islamiyya da aka yi garkuwa da su a Najeriya

An saki wasu daga cikin daliban Islamiyya da aka yi garkuwa da su a Najeriya

'Yan bindiga sun saki 11 daga cikin daliban Islamiyya sama da 100 da suka yi garkuwa da su a makarantarsu a jihar Niger.

Gwamnan jihar Niger Abubakar Sani Bello ya tunatar da cewa, 'yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai da dama a makarantar Islamiyya da ke yankin Tegina.

Bello ya ce, an saki yara kanana 11 daga cikin daliban da aka yi garkuwa da su saboda sun yi kankanta yadda ba za su iya tafiya ba.

Bello ya kuma ce, ana ci gaba da kula da lafiyar wasu mutanen sama da 10 da suka samu raunuka a lokacin da 'yan bindigar suka kai harin, kuma an fara aiyukan nemo daliban tare da kubutar da su.

Mutum 1 ya rasa ransa a lokacin da 'yan bindiga suka kai hari makarantar Islamiyya a yankin Tegina na jihar Niger a ranar Lahadin nan.

Jaridun Najeriya sun bayyana cewa, an yi garkuwa da sama da dalibai 100 a yayin kai harin.


News Source:   ()