An saki Sonko a Sanagal

An saki Sonko a Sanagal

A Sanagal an saki Shugaban Jam'iyyar PASTEF Ousmane Sonko wana aka tsare tun ranar 3 ga Maris bisa zargin sa da tayar da zaune tsaye.

An saki Sonko bisa sharuddan bibiyarsa bayan ya bayar da shaida a kotu game da zargin sa da yin fyade da kuma yin barazanar kisa.

An bayyana cewa, Sonko ya koma gida bayan sakin sa da aka yi.

A gefe guda, a wasu sassan Dakar an fara gudanar da zanga-zangar kwanaki 3 da aka shirya yi a fadin kasar.

An samu labarin yin arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga a kusa da jami'ar Cheikh Anta Diop da Parcelles.

A karshen makon da ya gabata ne 'yan adawa da kungiyoyin farar hula suka yi kira da a gudanar da zanga-zanga a fadin kasar Sanagal. Hakan ya sanya aka jibge sojoji a Dakar da kewaye tun daga daren Litinin din nan.

A wannan makon an sake tsaurara matakan tsaro saboda tunanin zanga-zangar za ta kara munana sosai.

Shafin Twitter na ofishin jakadancin Turkiyya a Dakar ya gargadi 'yan kasar da kar su fita waje a wannan lokaci matukar ba ta kama dole ba.

Sakamakon haka an dkatar da aiyuka a ofishin jakadancin a ranar Litinin din nan.

A gefe guda, mutane miliyan 1,3 ne suka yada gangamin #freesenegal da ake yi tsawon kwanaki 3.

'Yan wasa, mawaka, 'yankwallon kafa da sanannun mutane 'yan Afirka sun dinga yada gangamin a shafukan sada zumunta.

A daidai lokacin da hakan ke faruwa, tsohon Shugaban Kasar Sanagal Abdullahi Wade ya yi kira ga Shugaba mai cinMacky Salla da kar ya saurari Ministan Harkokin Cikin Gida Antoine Felix Diome.


News Source:   ()