A yankin arewa maso-gabashin Najeriya an saki 'yan ta'addar Boko Haram 600 da aka kama bayan sun tuba kuma aka ba su horon yadda za su dawo cikin al'umma lafiya.
Kakakin Farmakan "Safe Corridor" Bamidele Shafa ya shaida cewar an kama 'yan ta'addar a jihohin Borno, Adama da Yobe, kuma sun sun yi nadama inda bayan kammala samun kulawa aka sake su.
Shafa ya ce tsaffin 'yan ta'addar da aka saki sun rantse ba za su sake shiga kungiyar ba.
Kakakin ya kuma ce a baya ma an saki tsaffin 'yan Boko Haram da suka tuba su 1,400, a yanzu kuma akwai wasu 280 da ake ci gaba da ba wa horon yadda za su koma rayuwa mai inganci.