An saki fursunoni 180 a Mali

An saki fursunoni 180 a Mali

A Mali an sallami fursunoni 180 da ake tsare da su a gidan kurkuku.

Wani jami'in gwamnatin Mali ya bayyana cewar a ranar Asabar an sallami fursunoni 70, ranar Lahadi kuma 110 daga wani gidan kurkuku da ke Bamako Babban Birnin Kasar.

Mutanen 180 da ake zargin mambobin kungiyar ta'adda mai tsaurin ra'ayi ne, sun samu 'yanci a matsayin musaya don sakin dan adawa Soumaila Cisse da aka yi garkuwa da shi a watan Maris.

Kafin zaben ranar 29 ga Maris a Mali ne a lokacin da shugaban jam'iyyar URD Soumaila Cisse ya ke yakin neman zabe aka yi garkuwa da si tare da waus mutane 11 da ke tare da shi a kan hanyar Sarafere zuwa Koumaira.

An kashe mai tsaron lafiyar Cisse a musayar wutar da aka yi da 'yan bindigar da suka yi garkuwar da su.

Tun wannan lokaci zuwa yau ake tsare da Cisse.


News Source:   ()