An sake zabar Touadera a matsayin Shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

An sake zabar Touadera a matsayin Shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

An sake zabar Faustine Archange Touadera a matsayin Shugaban Kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a zaben da aka gudanar a ranar 27 ga Disamban 2020 bayan ya samu kaso 53,92 na kuri'un da aka jefa.

Kaso 76 na masu jefa kuri'a ne suka fita zaben.

Sauran 'yan kara sun hada da na jam'iyyar URCA Anicet-Georges Dologuele da ya samu kaso 21, sai na jami'yyar MLPC kuma tsphon Firaminista Martin Ziguele da ya samu kaso 7,4 inda wadda ta yi shugabancin rikon kwarya a tsakanin 2014-2016 Catherine Samba-Panza ta samu kaso 0,86 na kuri'un da aka jefa a zaben.

An yi zaben a cikin inuwar rikici, inda kusan masu jefa kuri'a miliyan 1,8 suka zabi Shugaban Kasa da 'yan majalisar dokoki 140 da za su shugabanci kasar na tsawon shekaru 5.


News Source:   ()