An sake yi wa mutane 800 allurar riga-kafin Corona ta bogi a Uganda

A kasar Uganda da ke gabashin Afirka an gano an sake yiwa wasu mutane 800 allurar riga-kafin Corona ta bogi.

Shugaban Kwamitin Sanya Idanu Kan Harkokin Kula da Lafiya Dr. Wallen Naamara ya sanar da cewa, yawaitar karuwar masu kamuwa da cutar a kasar na sanya fargaba sosai.

Naamara ya kara da cewa,

"Wasu da suke son samun kudi ta kowacce hanya suna yiwa jama'ar allurar riga-kafin Corona ta bogi."

Ya ce, a tsakanin watannin Mayu da Yuni an yi wa a kalla mutane 800 allurar riga-kafin Corona jabu a Uganda, wasun su ma ruwa aka zuba musu a matsayin allurar.

Naamara ya ce, tuni aka fara gudanar da bincike, kuma an kama ma'aikatan jinya 2, wani likita kuma ya ranta a na kare.

Naamara ya kara da cewa, kyauta ake yin allurar riga-gafin Corona a Uganda, kuma kar wanda ya bayar da kkudinsa don karbar allurar.

 


News Source:   ()