Wannan shi ne karo na 9 da ake samun bullar cutar a wannan kasa dake gabashin Afirka tun daga bullar cutar da aka gani a kasar a shekara ta 2000.
Rahotanni sun ce mutum na farko da ya kamu da cutar wani mai taimakawa likita ne a asibitin Mulago, kuma ya ziyarci wurare da dama domin samun magani cikin su harda masu bada maganin gargajiya.
Bayanai sun ce cutar ta yiwa mutumin illa wajen lalata wasu sassan jikinsa kafin ya rasu jiya laraba.
Yanzu haka hukumomin lafiya na bincike da kuma gano mutane 44 da ake zaton ya yi mu'amala da su domin musu gwaji, cikin su harda jami'an kiwon lafiya 30 kamar yadda hukumomin lafiyar kasar suka bayyana.
Sai dai masana na bayyana cewar gano wadannan mutane 44 zai yi wahala lura da yawan mutanen dake birnin Kampala wadanda yawan su ya zarce miliyan 4, baya ga zama hanyar mutanen dake fitowa daga kasashen Sudan ta Kudu da Congo da Rwanda da kuma wasu kasashen dake yankin.
Ita dai wannan cuta ta ebola ana yada ta ne ta hanyar mu'amala ko yawu ko zufa, kuma alamomin ta sun hada da ciwon kai da aman jini da kuma zubar jinin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI