An sake saka dokar hana fita a jihar Plateau

An sake saka dokar hana fita a jihar Plateau

Sakamakon rikice-rikicen da ake yi a jihar Plateau da ke arewa ta tsakiyar Najeriya, an sanar da dokar hana fita waje a jihar.

Kakakin Yada Labaran Gwamnatin Plateau Makut Macham ya shaida cewa, sakamakon hare-haren da ake ci gaba da kaiwa a jihar gwamna Simon Lalong ya saka dokar hana fita.

Macham ya ce, dokar hana fita wajen ta fara aiki a yankunan Zangam da Jos ta Arewa, kuma an dauki matakin don hana ci gaba da samun asarar rayuka da dukiyoyi.

Macham ya kara da cewa, wannan mataki zai taimaka wajen nemowa da kamo maharan.

 


News Source:   ()