Sojojin Faransa da ke aiki a Rundunar Farmakan Berkhane 2 sun rasa rayukansu sakamakon harin bam da aka kaiwa motarsu a Mali.
Wani sojan na Faransa 1 ya samu raunuka a harin da aka kai musu a yankin Meneka.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewar, yana jin irin radadin da iyalan sojojin su ke ji, kuma yana mika sakon ta'aziyya gare su.
A ranar 28 ga Disamba ma an kashe sojojin Faransa 3 da suke kai farmakan Berkhane a yankin Hombori na Mali da ke iyaka da kasashen Burkina Faso da Nijar.
Kungiyar Alka'eda a yankin Sahel ta dauki alhakin kai harin.
A karkashin farmakan Berkhane da Faransa ta fara kaddamarwa a shekarar 2014 a Murtaniya, Mali, Burkina Faso, Nijar da Chadi, ta aika da sojoji dubu 5,100 zuwa kasashen.