An sake gwabza fada a Kimbumba dake gabashin DRCongo

An sake gwabza fada a Kimbumba dake gabashin DRCongo

A yankin Sake an cimma zaman lafiya na gajeren lokaci,inda aka sake fuskantar tashin hankali  bayan jin karar  harbe-harbe a Kibumba da ke da tazarar kilomita 20 daga arewacin Goma a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.

Mazauna kauyen Rusayu da ke cikin kungiyar Muja, sun ba da rahoton cewa, an yi arangama, an ji karar harbe-harbe da manyan bindigogi da kuma kananan bindigogi da sanyin safiya, mai tazarar kilomita 20 daga Goma.

Taswirar Afrika mai nuna Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo. Taswirar Afrika mai nuna Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo. AFP

Wani harsashi da ya fado a gundumar Turunga ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula biyu. A bangaren Sake kuwa, layin gaba an cimma zaman lafiya da kwanciyar hankali a safiyar yau. A cewar majiyoyin cikin gida, Yan tawayen na M23 da ke samun goyon bayan dakarun sojojin Rwanda sun kasance a Sake mai tazarar kilomita ashirin daga Goma, babban birnin lardin, kusan duk ranar Alhamis. An yi ta musayar wuta har cikin dare. Dakarun DRC (FARDC) sun zafafa ayyukansu ta hanyar tura jirage masu saukar ungulu da wasu manyan makamai don dakile ci gaban wadannan mayaka (daga M23, da Rwanda ke goyon bayan).

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)