A garin Terhune na gabashin Libiya da dakarun kasar suka kubutar daga hannun 'yan tawaye mabiyar Haftar Khalifa a watan Yuni, an sake gano wani rami da aka binne mutane da dama a cikinsa.
Daraktan Hukumar Neman Mutanen da Suka Bata ta Libiya, Lutfi Tevfik ya shaida cewar, ya ce ramin da aka gano a Libiya an ciro jikkunan mutane 2, kuma ana tunanin adadin zai karu.
A ranar 25 ga watan Maris ne sojojin Libiya suka kaddamar da farmakan "Guguwar Zaman Lafiya" a kasar, sun kubutar da Tarabulus a ranar 3 ga Yuni, Terhune kuma a ranar 5 ga Yuni.
Tsawon shekaru 14 mayakan Haftar suka mamaye Terhune ,inda suke amfani da garin a matsay,n cibiyar albarkatun man da suke amfani da shi wajen kai wa Tarabulus hare-hare.