An sake gano jikkunan mutane 10 a garin Terhune na Libiya

An sake gano jikkunan mutane 10 a garin Terhune na Libiya

A garin Terhune na Libiya an sake gano jikkunan mutane 10.

Rubutacciyar sanarwar da aka fitar daga Hukumar Bincike da Nemo Mutanen da Suka Bata ta bayyana cewa, a yayin aiyukan haka a wata gona an sake gano wani rami da aka binne mutane da dama a garin Terhune da a 2020 aka kubutar daga hannun mayaka masu goyon bayan dan tawaye Haftar Khalifa.

An bayyana gano jikkunan mutane 10 a cikin kabarin, ya zuwa yanzu ba a gama tantance su waye mutanen da aka binne a ramin ba.

Ya zuwa yanzu an gano kaburbura 55 da aka binne mutane da dama a garin Terhune da kewaye.

Mahukuntan Libiya sun bayyana cewa, an samu jimillar jikkunan mutane 135 da aka binne a ramuka daban-daban a garin Terhune da kewaye.

A watan Yuli ma Hukumar Bincike da Nemo Mutanen da Suka Bata ta bayyana gano jikkunan mutane 15 a garin.


News Source:   ()