An sake gano garwakin mutane 5 a ramukan da aka binne mutane da dama a cikinsu a garin Terhune na Kudancin Libiya, wanda dakarun sojin kasar suka kwace daga hannun 'yan tawaye masu biyayya ga dan juyin mulki Haftar Khalifa a ranar 5 ga Yuni.
Rubutacciyar sanarwar da aka fitar daga Hukumar Bincike da Gano Wadanda aka binne ta ce a dazukan yankin Al-Ribat na kudancin Terhune an sake gano jikkunan mutane 5 a aiyukan haka da ake yi don gano adadin wadanda aka kashe tare da binnewa a ramuka guda.
A aiyukan hakar da ake yi a yankin Al-Ribat an ciro jikkunan mutane 10 a ranar 10 ga Yuni da gawarwaki 9 a ranar 28 ga Yuni wanda adadinsu ya kama 28 a yanzu.
Bayan da sojojin Libiya suka kwace iko da Terhune da ya zama cibiyar daukar man fetur da kai hare-hare a kudancin Libiya da dan tawaye Haftar ya dauki tsawon watanni 14 yana yi, an sanar da gano kaburbura 11 da aka binne mutane da dama a cikinsu.
A ranar 22 ga watan Yuni Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ta sanar da cewar kwararan bayanai sun isa gare ta da ke nuna an gano kaburbura 11 a yankin Terhune dauke da mutane da dama da aka binne a cikinsu.