An sake ciro gawarwakin mutane 6 a ramukan haƙar zinaren Afrika ta kudu

An sake ciro gawarwakin mutane 6 a ramukan haƙar zinaren Afrika ta kudu

Johannes Qankase kakakin shugaban ƙauyen na Stilfontein ya ce galibin mahaƙan sun fito ne daga ƙauyen Khuma da ke maƙwabtaka da yankin kuma anyi nasarar ɗakko gawarwakin na su ne tsakanin kwanaki biyu daga jiya zuwa yau.

Yasasshiyar mahaƙar zinaren mai tazarar kilomita 150 daga kudu maso yammacin birnin Johannesburg tsawon makwanni 4 ta shafe ta na fuskantar ƙawanyar jami’an ƴan sanda da ke da nufin tilastawa dubunnan mahaƙan da ke maƙale a ƙarƙashin ƙasa fitowa daga rami.

Masu aikin haƙar da ake kira "zama zamas" da harshen Zulu wato waɗanda suka ƙoƙarta, kai tsaye mahukuntan Afrika ta kudu na kallonsu a matsayin waɗanda ke haramtacciyar harƙalla.

Zuwa yanzu gawarwakin mutane 7 aka fitar daga ramukan haƙar zinaren tun bayan faro aikin rarakar mutanen daga cikin ramuka.

Bayanai sun ce akwai mahaƙa aƙalla dubu 4 da ke cikin ramukan haƙar zinaren, kuma galibinsu sun fito ne daga ƙasashen Mozambique da kuma Lesotho.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)