An sake bude makarantu 10 a jihar Kwara ta Najeriya bayan takaddamar sanya Hijabi

An sake bude makarantu 10 a jihar Kwara ta Najeriya bayan takaddamar sanya Hijabi

An sake bude wasu makarantu 10 a jihar kwara da ke Najeriya bayan da aka rufe su na wani lokaci sakamakon nuna adawa da sanya Hijabi da dalibai mata ke yi.

Babbar Sakatariya a Ma'aikatar Ilimi ta jihar Kwara Mary Adeosun ta shaida cewa, sakamakon umarnin da gwamnan jihar Abdurrahman Abdurrazak ya bayar an sake bude makarantun goma da ke Ilorin a ranar Litinin din nan.

Adeosun ta kara da cewa, an dauki dukkan matakan tsaro da suka kamata don ganin daliban sun shiga azuzuwa tare da daukar darussa lafiya.

Gwamnatin Kwara ta kawo karshen muhawara da takaddama da ake yi game da sanya hijabi a makarantun jihar inda ta ce, daga 26 ga Fabrairun 2021 dalibai mata na da 'yancin saka Hijabi.

Musulman da ke jihar sun yi maraba da wannan mataki, amma Kiristoci ba su yi murna ba.

A ranar 8 ga Maris aka rufe makarantu 10 da ke jihar Kwara saboda yadda aka kasa cimma matsaya tsakanin Malaman Musulunci da na Kiristanci kan sanya Hijabin.

A ranar 17 ga Maris aka bude makarantun jihar inda sakamakon yadda aka hana wata yarinya shiga makaranta da Hijabi rikici ya barke tare da jikkata mutane 5.


News Source:   ()