An sake arangama tsakanin ƴan sandan Kenya da masu buƙatar murabus ɗin Ruto

An sake arangama tsakanin ƴan sandan Kenya da masu buƙatar murabus ɗin Ruto

Masu zanga-zangar a yammacin yau Alhamis sun tsananta kiraye-kirayen ganin shugaba William Ruto ya yi murabus daga kujerar mulkin ƙasar ta gabashin Afrika, lamarin da ya sanya jami’an ƴan sandan ci gaba da gwabza arangama da su tare da fatattakarsu daga tsakiyar birnin Nairobi fadar gwamnati. 

Yanayin zanga-zangar na yau da aka yiwa laƙabi da "Nane Nane" wato takwas takwas da ke nufin kwanan watan 8 ga watan Agusta, kai tsaye ya sauya salo daga yanayin gangamin da ƙasar ta shafe makwanni ta na gani, inda a yau kai tsaye masu gangamin ke buƙatar murabus ɗin shugaba Ruto maimakon neman sauƙin rayuwa da sassauci kan halin da al’umma ke ciki.

Zuwa yanzu mutane fiye da 50 suka rasa rayukansu tun bayan faro zanga-zangar da matasa suka yi a watan Yuni da nufin tilastawa gwamnati janye wasu manufofinta da suka haddasa matsi da tsadar rayuwa.

A ɓangare guda ƙungiyar ƴan jaridu ta ƙasa da ƙasa RSF ta yi zargin jami’an tsaron Kenyan da keta haddi baya ga yin karan tsaye ga kariyar da ƴan jarida ke da shi ta yadda suka yi amfani da hayaƙi mai sanya hawaye baya ga harsasan roba kan ƴan jaridar da ke bakin aiki.

Ƙungiyar ta kuma zargi jami’an tsaron da kame tarin ƴan jarida a wani yunƙuri na tilasta musu yin gum da baki ko kuma kaucewa ɗaukar rahoto kan halin da ake ciki yayin zanga-zangar.

A gangamin na yau Alhamis kaɗai ƴan sandan Kenya sun kame mutane 174 ciki har da 126 a birnin Nairobi, yayinda suka jikkata ƴan jarida 3 kamar yadda ƙungiyar ƴan jaridun ƙasashen gabashin Afrika ta wallafa a shafinta na X.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)