Sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku a jihohin Jonglei da Pibor na kasar Sudan ta Kudu, an aiyana dokar ta baci.
Kakakin Fadar Shugaban Kasar Ateny Wek Ateny ya fitar da sanarwa game da ibtila'in.
Ya ce "Manufar sanya dokar ta bacin ba wai barin wadanda lamarin yashafa cikin mawuyacin hali ba ne, manufar ita ce a taimaka musu."
Ya kara da cewar Ma'aikatar Magance Annoba da Bayar da Agaji za ta taimakawa wadanda ambaliyar ruwan ta tagayyara.
Mutane da dama sun rasa rayukansu a Sudan ta Kudu sakamakon ambaliyar ruwan.
Ana bayyana cewar sama da mutane dubu 150 sun rasa matsugunansu a kasar.