An saka dokar hana fitar a jihar Gombe da ke arewa maso-gabashin Najeriya sakamakon rikicin addini da na kabilanci da ake ci gaba da samu a jihar.
Sakataren Gwamnatin jihar Gombe Ibrahim Abubakar ya sanar da cewa, an aiyana dokar hana fita sakamakon rikicin da ya barke tsakanin wasu bangarori a yankin Balanga.
Abubakar ya ce, "Sakamakon rikicin da aka samu a kauyukan Nyuwar, Jessu da Yolde an saka dokar hana fita."