Wasu 'yan bindiga da ake zatun masu kame mutane ne domin karbar kudin fansa sun kai hari a wani Masallaci dake jihar Zamfara dake Najeriya inda suka kashe mutum 5 da kuma yin awon gaba da 40.
Maharan da ba'a san ko su wanene ba sun bayyana a Masallacin ne saman babura.
Tuni dai jami'an tsaro sun kewaye yankin inda suka fara bincike akan lamarin.
A jihar Zamfara dai an dauki kusan shekaru hudu ana dauki ba dadi tsakanin manoma da makiyaya.
A yayinda makiyaya ke zargin ana sace musu dabbobi, manoma na zargin makiyaya na lalata musu amfanin gona.
A yankin dai an bayyana cewa an kashe kusan mutum dubu biyu inda dubbai kuma suka rasa mastugunansu sakamakon rikicin.