A wasu farmakai da aka kai wa 'yan ta'addar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, an lalata sansaninsu tare da kashe 'yan ta'addar da dama.
Kakakin Ma'aikatar Tsaro John Enenche ya shaida cewar bayan da 'yan ta'addar Boko Haram suka kai hari a Zabarmari da ke jihar Borno a karshen makon da ya gabata, sojoji sun fara kai musu farmakai a dajin Sambisa.
Enenche ya ce, an lalata mafakar 'yan ta'addar tare da kashe wasu da sama daga cikinsu.