An rusa makarantu dubu 7 a Itopiya

An rusa makarantu dubu 7 a Itopiya

Makarantu dubu 7 ne suka rushe sakamakon rikicin da dakarun sojin Itopiya suke yi da Mayakan yankin Tigray na (TPLF).

Ministan Ilimi na Itopiya Getahun Mekuria ya zanta da manema labarai a Addis Ababa cewa, mayakan TPLF sun rusa gaba daya ko lalata wani bangare na makarantu dubu 7.

Mekuria ya kara da cewa, a wata dayan da ya gabata, mayakan TPLF sun rusa makarantu 455 da ake koyar da dalibai dubu 88 a cikinsu.

Mayakan TPLF na ci gaba da kutsa kai zuwa jihohin Afar da Amhara da ke arewacin Itopiya.

Mayakan na TPLF da suka shiga garin Lalibela mai tarihi, suna kuma gwabza fada da mayakan tarayya domin kwace garin Weldiya.

A watan Nuwamban 2020 dakarun Itopiya suka fara kai farmakai yankin Tigray inda a ranar 28 ga Yunin 2021 suka janye daga Mekelle Babban Birnin yankin.

Bayan da Firaminista Abiy Ahmed ya hau karagar mulki a shekarar 2018 ne mayakan TPLF suka fara rikicin siyasa da jam'iyyun da suke wakiltar gwamnati wadanda mabiyansu suka fito daga kabilun Amhara da Oromo mafi yawa a kasar.


News Source:   ()