An rufe makarantu 10 na wani dan lokaci a jihar Kwara ta Najeriya saboda takaddama kan daliban da suka sanya hijabi.
Kemi Adesun, Babban Sakatare a Ma’aikatar Ilimi da Ci Gaban Dan Adam ya bayyana cewar an yi muhawara tsakanin Musulmai da Kirista a kan daliban da ke sanya hijabi a makarantu a jihar Kwara.
A dalilin haka ne, Adesun ya bayyana cewar an rufe makarantu 10 na wani dan lokaci a yankin Ilorin sannan kuma gwamnati ta yi kira ga mazauna yankin da su zauna lafiya kuma ya kamata iyaye da shugabannin addinai su guji aikatawa da maganganun da ke iya kara raba kan kungiyoyin biyu.
A yankunan kudu da yamma inda galibi kiristoci ke zama, batun amfani da hijabi a wasu makarantu abun tattaunawa a kai ne.
A cikin jihar Oyo a shekarar 2018, an kori dalibai 9 daga makaranta saboda sanya hijabi.