Sakamakon bukatar da Turkiyya gabatar, an rufe makarantar 'yan ta'addar Fethullah (FETO) da ke kasar Togo
https://www.trt.net.tr/hausa/afirka/2021/06/02/an-rufe-makarantar-yan-ta-addar-feto-a-togo-1650546
Ministan Harkokin Waje da Kula da 'Yan Kasar Togo Mazauna Kasashen Ketare Robert Dussey ya ziyarci Ankara tare da gudanar da taron manema labarai da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu.
Dussey ya sanar da cewa, sakamakon bukatar da Turkiyya ta gabatar, an rufe makarantar 'yan ta'addar FETO da ke Togo.
Dussey ya kara da cewa, tare da taimakon Turkiyya da Asusun Ma'arif, za a ci gaba da bawa daliban makarantar ingantaccen ilimi.
Ministan na Togo ya bayyana za su bude ofishin jakadanci a Ankara.
Haka zalika ya kuma ce, suna jiran 'yan kasuwar Turkiyya a Lome, kuma yana sa ran kafin wannan shekarar ta kare za a gudanar da taron Ranar Turkiyya-Togo wanda hakan zai taimaka wajen a bayyanawa 'yan kasuwar Turkiyya damarmakin da ake da su a Togo.