Akalla makarantu 618 aka rufe a arewacin Najeriya sakamakon hare-haren 'yan bindiga da ke kara yawaita a yankin.
Sakamakon yadda a 'yan kwanakin nan ake kai hare-hare a makarantu tare da garkuwa da malamai da dalibai, an rufe akalla makarantu 618 a jihohin Sokoto, Zamfara, Kano, Niger, Katsina da Yobe.
Kwamishin Harkokin Tsaro na jihar Sokoto Garba Moyia ya bayyana cewa, sun dauki wannan mataki ne saboda yadda ake garkuwa da dalibai a arewacin Najeriya.
Moyia ya kara da cewa, ana ci gaba da aiyukan nemo daliban da aka yi garkuwa da su a yankunan.
Daga watan Janairu zuwa yau an yi garkuwa da dalibai a makarantu 5 a Najeriya.
Lamari na karshe ya afku a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna inda aka yi garkuwa da daliban makarantar firamare da dama da malamansu 3.