An rantsar da shugaban ƙasar Mozambique Chapo a wani yanayi na rikicin siyasa

An rantsar da shugaban ƙasar Mozambique Chapo a wani yanayi na rikicin siyasa

Samun nasarar Daniel Chapo mai shekaru 48 a zaɓen, ya tsawaita wa'adin mulkin jam'iyyarsa ta Frelimo na tsawon shekaru 50 na mulkin kasar Afirka mai arzikin iskar gas a daidai lokacin da babban abokin hamayyarsa  Venancio Mondlane ke cewa an tafka magudi a zaben.

A yayin da ikrarin na Mondlane ya haifar da tarzoma da wata kungiya mai zaman kanta ta ce ta yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 300.

Mondlane dake bugun ƙirjin shike jan akalar matasa a ƙasar ya sha alwashin haifar da tafiyar ƙaguwa ga alƙiblar sabuwar gwamnatin ƙasar ta hanyar shirya da shirya zanga-zangar da zata rikita tunanin masu mulkar ƙasar.

Sai dai a wani bangare kuma wasu ƙasashe 16 dake kudancin Afirka sun yi kira na ganin ƴan adawa sun kiyayi ta da hankali a yayin da sabuwar gwamnatin ke gudanar da lamuranta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)