Bayan rantsuwar kama aikin da ya samu halartar daruruwan mutane, ciki harda shugabanin wasu kasashe, shugaban ya yi jawabin dake gargadi ga manyan kasashen duniya da su kaucewa tirsasawa kasashen Afirka yin abinda suke so.
A matsayin mu na ƙasashen dake cikin duniya, muna da abubuwan da suka hada mu fiye da yadda muke tunani, kuma a tsakanin mu, muna da damar da za mu iya gyara, wannan bai zama cewar dole mu cimma yarjejeniya a kan komai ba, amma dole mu mutunta abinda kowane bangare ya zaba, dukkanmu.
Shugaba Kagame da ya ce babu wata dama da manyan kasashen duniya ke da shi na tilasta abinda suke so su ga sauran ƙasashe sun bi, ko kuma su kirkiri karya domin boye gaskiyar lamura.
Shugaban ƙasar Rwanda Paul Kagame yayin rantsuwar kama aiki. 11/08/24 REUTERS - Jean BizimanaTo sai dai makusancin makwabcinsa, shugaban Kongo, Felix Tshisekedi bai halarci bikin rantsuwar ba, kuma hakan baya rasa nasaba da taƙun tsaka da ke tsakanin shugabannin biyu kan zargin taimakawa ƴan tawayen M23.
Mista Kagame ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a watan da ya gabata da fiye da kashi 99 cikin 100 a takarar da aka haramta wa mafiya wayan 'yan adawa tsayawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI