An rantsar da Kithure a matsayin sabon mataimakin shugaban ƙasar Kenya

Babbar kotu a Kenya ce ta dakatar da rantsar da Kindiki bayan Gachagua da magoya bayansa sun shigar da ƙarar ƙalubalantar tsigeshi da majalisun dokokin ƙasar biyu suka yi.

To sai dai  a ranar Alhamis kotu ta janye dakatarwar da aka yi na rantsar da Rigathi Gachagua a matsayin sabon mataimakin shugaban ƙasar Kenya.

Umurnin Kotun Ƙoli

Kotun ƙoli a Kenya ce ta bayar da umarnin rantsar da sabon mataimakin shugaban ƙasa, bayan majalisun dokokin ƙasar biyu suka tsige Rigathi Gachagua daga muƙaminsa.

An dai share tsawon watanni ana fama da rikici tsakanin Shugaba William Ruto da mataimakinsa Rigathi Gachagua, to sai dai a ranar 17 ga watan oktoban da ya gabata rikicin ya ɗauki sabon salo inda har ta kai ƙarama da kuma babbar majalisar dokokin dokokin ƙasar suka kaɗa ƙuri’ar kawo ƙarshen mulkinsa.

Wanda ake shirin rantsarwa a wannan juma’a wato ministan cikin gida Kithure Kindiki, mutum ne mai shekaru 52 a duniya, kuma ya yi fice saboda kasancewarsa kasaitaccen malamin jami’a, kafin daga bisani ya tsunduma siyasa daga-gadan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)