Boko, mai shekaru 54, ya karɓi rantsuwar ce a gaban dubban mutane a babban filin wasannin motsa jiki na kasa kwanaki tara bayan da jam’iyarsa ta UDC ta yi nasara akan jam'iyyar Botswana Democratic Party BDP.
A yayin da Boko ke cewa "Kusan shekaru uku da suka gabata, dimokuradiyyar mu ta samu gindin zama amma kuma maras tabbas, sannan mun fafata a ranar 30 ga watan Oktoban bana tare da abokan hamayyar mu kuma muka yi nasara a kansu.
Jam'iyyar UDC mai tsaka-tsakin ra’ayi ta Boko ta lashe kujeru 36 a majalisar dokokin kasar idan aka kwatanta da abinda jam'iyyar BDP mai ra'ayin mazan jiya ta samu inda ta ƙare da kujeru 4.
Tsohon shugaban kasar ta Botswana Mokgweetsi Masisi, wanda ya amince da shan kaye kwanaki biyu bayan kada kuri'ar, ya kasance a cikin mahalarta taron haɗa ka da shugabannin wasu kasashen kudancin Afirka da suka hada da Namibiya, Zambia da Zimbabwe suka gudanar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI