Mutane sama da dubu 27 aka raba da matsugunansu a shekara dayan da ta gabata sakamakon rikice-rikice a jihar Kaduna da ke arewa maso-yammacin Najeriya.
Kwamishinan Hukumar Kula da 'yan Gudun Hijira ta Najeriya Sanata Bashir Garba Muhammadya bayyana cewa, sakamakon rikice-rikicen da ake samu a yankin Birnin Gwari na jihar kaduna, a shekara dayan da ta gabata an raba sama da mutane dubu 27 da matsugunansu.
Muhammad ya bayyana cewa, mafi yawan wadanda aka raba da matsugunan nasu mata ne da yara kanana, kuma gwamnati aike musu da kayan abinci da na amfanin yau da kallum.
Sakamakon yadda 'yan bindiga ke amfani da babura wajen kai hare-hare ya sanya aka hana amfani da babur a wasu jihohin.