An nemi wani dan jaridar Masar an rasa a kan hanyarsa ta zuwa Alkahira daga Istanbul

An nemi wani dan jaridar Masar an rasa a kan hanyarsa ta zuwa Alkahira daga Istanbul

Rahotanni sun ce an nemi mamban kungiyar 'yan jaridu ta Masar Jamal Al-Jamal an rasa a kan hanyarsa ta tafiya Alkahira daga Istanbul.

Wasu bayanai na cewa, an kama dan jaridar a filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa da ke Alkahira, kuma ba a san ina aka kai shi ba.

Kungiyar Larabawa da ke Ingila ta sanar da cewa, iyalan Al-Jamal sun bayyana mata cewar, bayan ya isa Al-Kahira a ranar 22 ga Fabrairu, ba a sake jin duriyarsa ba.

Sanarwar ta tunatar da cewa, a shekarar 2014 Al-Jamal ya yi rubutu a wata jarida mai suna Al-Yaum inda ya soki gwamnatin Masar, kuma a wannan lokacin Shugaban Masar Abdulfatah Al-Sisi ya kira shi a waya tare da gargadar sa.

Bayan Al-Jamal ya tattauna da Sisi ta wayar tarho ne ya dawo Turkiyya da zama.

Wasu 'yan jaridar Masar sun tabbatar da an kama Al-Jamal tare da daure shi, sun kuma yi kira ga mahukuntan kasar da su sake shi ba tare da bata lokaci ba.

 


News Source:   ()