Bayan juyin mulkin ranar 18 ga watan Agusta, an nada Kanal Bah N'Daw mai ritaya a matsayin Shugaban Kasa na rikon kwarya a kasar Mali, wanda hakan ya janyo cece-kucen ko shugaba ne na soja ko na farar hula.
Majalisar Sojoji 'Yan Juyin Mulki ta Mali sun sanar da cewar sun cimma matsayar nada tsohon soja, kuma tsohon Ministan Tsaro Kanal N'Daw a matsayin Shugaban Kasa na rikon kwarya.
Hukuncin Majalisar ya kuma bayyana shugaban CNPP Assimi Goita a matsayin mataimakin Shugaban Kasa.