A karon farko a Uganda an nada mata a matsayin Mataimakiyar Shugaban Kasa da kuma Firaminista.
A yayin rantsar da sabuwar majalisar zatarwar Uganda a Kampala, Shugaba Yowere Museveni ya rantsar da Jessica Alupo a matsayin Mataimakiyar Shugaban Kasa da Robinah Nabbanja a matsayin Firaminista.
A jawabin da Alupo ta yi bayan rantsuwar ta bayyana za ta yi iya kokarinta wajen magance matsalar talauci da ke damun jama'ar kasar.
Firaministan Nabbanja kuma ta shaida cewa, za ta yi hidima ga dukkan jama'ar Uganda ba tare da jin tsoro ba.
Mata 'yan siyasa, 'yan kasuwa, malaman jami'a da shugabanni a Uganda sun nuna gamsuwa kan yadda Museveni ya baiwa mata wadannan manyan mukamai.