An mikawa Somaliya allurar riga-kafin Korona fiye da dubu 302

An mikawa Somaliya allurar riga-kafin Korona fiye da dubu 302

Somalia ta karbi alluran riga-kafin Korona dubu 302,400 da kamfanin magunguna na Amurka Johnson & Johnson (J&J) ya samar  domin yaki da sabon nau'in cutar coronavirus (Kovid-19).

Dangane da labaran da manema labarai na kasa suka rawaito, allurai dubu 302 da dari 400 na alluran rigakafin Kovid-19, na (COVAX), an mika su ga hukumomin Somaliya.

Ministan lafiya na Somaliya Doctor Fevziye Abikar Nur, ta bayyana cewa akwai gwagwarmaya da lokaci wajen yaki da annobar da yiwa mutane allurar rigakafi, ta kara da cewa alluran da aka bayar suna da matukar muhimmanci.

An kai allurai 108,000 na Kovid-19 zuwa Somalia a makon da ya gabata.


News Source:   ()