Ɗan marigayi Gaddafi ya ce mahaifinsa ya taimaka wa Sarkozy a yakin neman zaɓe

Ɗan marigayi Gaddafi ya ce mahaifinsa ya taimaka wa Sarkozy a yakin neman zaɓe

Yayin tattaunawarsa da sashen faransanci na RFI, Saïf al-Islam Kadhafi ya amince da amsa tambayoyin manema labarai karon farko tun bayan bayyanar zargin a shekarar 2011, kuma hakan na zuwa ne makonni biyu da soma gudanar da shari’a a kan tsohon shugaban na faransa Nicolas Sarkozy tare da wasu mukarrabansa 11 a birnin Paris.

A cikin shaidar da ya bayar wadda ke rubuce a harshen larabci, Saïf al-Islam ya bayyana cewa yayin wani taro da ya gudana a birnin Tripoli,  ranar 6 ga watan Oktoban 2005, Sarkozy da Kadhafi sun tattauna batun samun gudumawar kudin da adadinsu ya kai euro miliyan 2 da rabi, dan yin amfani da su wajen yakin neman zaben shugabancin Faransa, sannan ya kara da cewa tsohon ministan cikin gida da kan shi , Claude Guéant ya tafi da gundarin kudin Faransa.

Dan tsohon shugaban na libya ya kara da cewa karon farko a shekarar 2021, an nemi ya karyata dukkannin zarge zargen da ake yi wa Nicolas Sarkozy, sannan ya ce a madadin haka aka alkawarta janye dukkannin tuhume tuhumen da ake masa a kotun hukunta manyan  laifuka ta duniya.

Saif ya kuma ce a karshen shekarar 2022, Sarkozy ya sake aika wa iyalansa wani jami’in diflomasiya, inda ya kawo batun kaninsa Hannibal Kadhafi da ya shafe tsawon shekaru tsare a Lebanon, dan ganin ya janye batun bada shaida a kansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)