An kubutar da Turkawa 15 da aka yi garkuwa da su a Najeriya

An kubutar da Turkawa 15 da aka yi garkuwa da su a Najeriya

An kubutar da Turkawa 15 ma'aikatan jirgin ruwa wadanda aka yi garkuwa da su a gabar tekun Najeriya a ranar 23 ga Janairu.

An bayyana cewar, mutanen na cikin koshin lafiya.

'Yan fashin teku ne suka yi garkuwa da mutane 15 daga cikin 19 a gabar tekun Najeriya bayan tashin su a cikin jirgin ruwan kamfanin Morealis mai suna Mozart daga Legas zuwa Cape Town.

A ranar 28 ga Janairu aka samu damar magana da 'yan fashin tekun, kuma sai a ranar Juma'ar nan aka samu labari mai dadi.

An kubutar da Turkawan 15 ma'aikatan jirgin ruwan bayan aikin da aka yi daga garin Hamburg na Jamus.

Jami'in kamfanin da ya zanta da atshar TRT Haber, Levent Karsan ya fadi cewa,

"Ma'aikatan jirgin ruwa Turkawa na Najeriya kuma suna nan kalau, bayan kammala tantance lafiyarsu za a kawo su Turkiyya."

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya ce, za su dakko Turkawan 15 daga Abuja zuwa Turkiyya a jirgin saman Turkish Airlines.

Cavusoglu ya ce, 'yan kasarsa na cikin kyakkyawan yanayi.


News Source:   ()