Rundunar sojin Najeriya ta sanar da kai farmakai kan 'yan ta'addar Boko Haram a arewa maso-gabashin kasar.
Kakakin Rundunar Sojin Sagir Musa ya shaida cewar jami'ansu sun kai farmaki kauyen Muktu da ke jihar Borno.
Sagir ya ce a yayin farmakin sun kubutar da yara kanana 38 da mata 34 da 'yan ta'addar Boko Haram suka yi garkuwa da su.
Ya ce an kashe 'yan ta'adda 18 inda wasu da dama suka gudu dauke da raunukan da suka samu, sojoji 2 sun mutu yayinda wasu biyu suka jikkata a yayin kai farmakin.
Ba a bayyana yaushe ne aka yi garkuwa da mutanen da aka kubutar ba.