A Najeriya, an kubutar da wasu mutane 18 da suka hada da mata da yara kanana daga hannun 'yan bindigar da suka yi garkuwa da su.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Rivers Nnamdi Omoni ya sanar da cewar sun kai farmakai kan 'yan bindiga da ke yankin Owerri na jihar bayan sun kai hari.
Omoni ya ce sakamakon farmakin, sun samu nasarar kubutar da mutane 18 da suka hada da mata da yara kanana daga hannun 'yan bindigar.
Ya ce an kashe 'yan bindiga 3 tare da kama wani daya, an kuma kwace makamai da yawa daga hannunsu.
Ba a bayyana yaushe ne aka yi garkuwa da mutanen ba.