A arewa maso gabashin Najeriya an kubutar da mutane 17 da 'yan ta'addar Boko Haram suka yi garkuwa da su.
Kakakin Rundunar Sojin Najeriya Onyema Nwachukwu ya shaida cewa, a kauyen Auno da ke jihar Borno ne 'yan ta'addar Boko Haram suka yi yunkurin kai hari wanda jami'an soji suka kawar.
Nwachukwu ya kara da cewa, bayan kawar da yunkurin kai harin aka kaiwa 'yan ta'addar Farmaki a hanyar Maiduguri-Damaturu inda aka kubutar da mutane 17 da kungiyar ke tsare da su.
Ya ce, mutanen na cikin yanayin lafiya mai kyau, kuma an mika su ga gwammnatin jihar Borno.