An kubutar da mutane 16 daga hannun 'yan bindiga a jihar Kaduna da ke Najeriya.
Kwamisinan Harkokin Cikin Gida da Tsaro na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya shaida cewa, an dakile yunkurin 'yan bindiga na kai hari a yankin Jem na jihar.
Aruwan ya kara da cewa, a farmakin da aka kai musu an kubutar da mutane 16 da 'yan bincigar suka yi garkuwa da su, an kuma kassara da yawa daga cikinsu.
Ba a bayyana yaushe aka yi garkuwa da mutanen ba.