An kubutar da mutane 16 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Delta da ke kudu-maso kudancin Najeriya.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Delta Ari Muhammad Ali ya bayyana cewar, an kaiwa 'yan bindiga da ke jihar 'Farmakin Sanity Sahel'.
Ali ya shaida cewa, a yayin farmakin an kubutar da mutane 16 da 'yan bindigar suka tsare bayan garkuwa da su.
Kwamishina Ali ya kara da cewa, an kuma kassara 'yan bindiga 2 a yayin kai farmakin, da yawan su kuma sun gudu da raunuka a jikkunansu.
Ali ya kum fadi cewa, za su ci gaba da gudanar da bincike don kamo 'yan bindigar, an kuma kwace makamai, babu da kayan aikin 'yan bncigar.