A Najeriya, an samu nasarar kubutar da fasinjoji 18 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a makon da ya gabata a jihar Niger.
Kakakin gwamnan jihar Niger Mary Noel-Berje ta sanar da cewa, a ranar 14 ga Fabrairu ne yan bindigar suka yi garkuwa da fasinjoji a hanyar Minna-Kontagora.
An bayyana cewa, ana ci gaba da kokarin ganin an saki daliban makarantar sakandire ta Kagara da aka yi garkuwa da su a ranar 17 ga Fabrairu.
Maharan sun kai hari kan makarantar tare da yin garkuwa da dalibai 27 da malamai 3 inda suka kashe wasu dalibai 2.
A 'yan shekarun nan, masu garkuwa da mutane na kai hari tare da yin awon gaba da jama'a don neman kudin fansa a Najeriya.