An kubutar da dalibai 180 daga cikin 210 da aka sace a Kaduna

An kubutar da dalibai 180 daga cikin 210 da aka sace a Kaduna

An sanar da nasarar kubutar da dalibai 180 daga cikin 210 da aka sace da suka hada da mata 42 da malamai 8 a jihar Kaduna dake kasar Najeriya.

Shugaban 'yan sandan jihar Kaduna Samuel Aruwan, ne ya sanar da kai hari a makarantar gandun daji dake yankin Mando inda aka sace akallan mutum 210.

Aruwan, ya bayyana cewa an kubutar da mutum 180 da suka hada da dalibai mata 42 da malamai 8 a farmakan da aka gudanar.

Daga cikin wadanda aka kubutar akwai wadanda suka ji raunuka kuma an fara kula da lafiyarsu kawo yanzu kuma ana cigaba da neman dalibai 30.

A bara a jihar Kaduna kawai sakamakon hare-haren bindiga da aka kai mutum 937 sun rasa rayukansu inda kuma aka sace 1972.

A kasar Najeriya daga watan Janairu kawo yanzu an kaiwa makarantu uku hari lamarin da ya sanya baiwa 'yan makaranta hutu a wasu jahohin dake arewacin kasar.


News Source:   ()