An kubutar da bakin haure 95 ‘yan kasashe daban-daban a lokacin da kwale-kwalensu ya kife a gabar tekun lardin Mednin na Tunisiya.
Daraktan Kungiyar Red Crescent na lardin Mednin na Tunusiya, Munci Selim ya bayyana cewa jami’an tsaron teku sun gano cewa jirgin ruwan da ke dauke da bakin haure a gabar tekun Cercis na lardin na da matsala.
Selim ya bayyana cewa an kubutar da 'yan Sudan 59, ‘yan Siriya 17, ‘yan Masar 7, 'yan Bangladesh 6, 'yan Guinea 3, 'yan Gana 2 da dan ci-ranin Tunisiya daya a cikin jirigin ruwa.
Da yake bayanna cewa bakin hauren da ake magana a kai sun tashi daga garin Sabrata da ke Libiya a jiya, Selim ya ce an kai wadanda ke cikin kwale-kwalen zuwa tashar Cercis kuma za a tura su zuwa Hukumar Kula da Shige da Fice don killace su.
Tunusiya, ƙaramar ƙasar Arewacin Afirka ta yi fice a matsayin matattarar baƙin haure da ke son zuwa Turai daga Afirka ta hanyar "cin gajiyar" tsarin tafiyar da abubuwa da fa'idar ƙasa tun daga shekarar 2011.