An kubutar da 'yan gudun hijira 80 a Saharar Jamhuriyar Nijar

An kubutar da 'yan gudun hijira 80 a Saharar Jamhuriyar Nijar

Jami'an Hukumar Yaki da Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM) sun kubutar da wasu 'yan gudun hijira ba bisa ka'ida ba su 80 da aka zubar a saharar Jamhuriyar Nijar.

An bayyana cewar masu fataucin mutane sun zubar da 'yan gudun hijirar da ke cikin motoci 4 bayan samun labarin ganin motar sojoji a yanki ma nisan kilomita 230 daga garin Dirkou na Nijar.

An bayyana cewar 'yan gudun hijirar sun kwashe kwanaki 3 ba tare da cin abinci da shan ruwa ba, kuma jami'an na IOM sun gano su ne a lokacin da suke yin ran gadi a sahara.

'Yan gudun hijirar da suka hada da yara kanana, sun fito daga kasashen Najeriya, Togo, Gana da Mali. An kuma kai su cibiyar kula da masu dauke da cutar Corona da ke yankin.

Za su zauna tsawon kwanaki 14, sannan daga baya za a Hukumar ta IOM ta mayar da su zuwa kasashensu.

Garin Dirkou na yankin Agadez da ke arewacin Jamhuriyar Nijar ne mafakar 'yan gudun hijirar Yammacin Afirka da ke son tafiyar Turai.

'Yan gudun hijirar na zama na tsawon kwanaki a Agadez kafin su tafi zuwa kasar Libiya.


News Source:   ()