An kubutar da 'yan gudun hijira 178 da jirgin ruwansu ya lalace a gabar tekun garin Medenin da ke kudu maso-gabashin Tunisiya.
Sanarwar da aka fitar daga Kungiyar Bayar da Agaji ta Red Crescent da ke Tunisiya ta ce, dakarun ruwa na kasar ne suka gano jirgin ruwa ya lalace a lokacin da suke yin sintiri a gabar tekun garin Medenin.
An gano gawarwakin mutane 2 a cikin jirgin, an kubutar da wasu mutanen 178. An bayyana cewa, bakin hauren sun fito ne daga kasashen Bangaladash, Masar da wasu kasashen Afirka.
Ba a bayyana dalina da suka yi ajalin mutane 2 da suka mutu ba.