A watan jiya ne shugaba Kiir ya amince da komawa tattaunawar sai dai ya bayyana cewa, sabuwar tattaunawar ba za ta ɗora kan yarjejeniyar shekarar 2018 face fatan ta samar da wata turba da za ta magance rikicin da ƙasar ke fuskanta tare da tilastawa tsageru miƙa wuya.
Yarjejeniyar Tumaini da aka samar a shekarar 2018 ta taimaka wajen kawo ƙarshen yaƙin basasar da Sudan ta kudu ta yi fama da shi wanda ya ɓarke lokaci ƙanƙani bayan samun ƴancin ƙasar yaƙin da ya hallaka mutanen da yawansu ya haura dubu 400.
Tun farko an dawo da tattaunawar fatan sake ƙulla yarjejeniyar ta Tumaini a watan Mayun shekarar nan amma aka dakatar da zaman bayan da shugaba Salva Kiir ya kori jami’an da ke wakiltar gwamnati a zaman.
Duk da cewa Kiir ya naɗa sabbin jami’an da za su wakilci gwamnati a zaman tattaunawar amma gayyata ta biyu kenan Nairobi na tura musu ba tare da sun bayyana don ci gaba da zaman ba, haka zalika babu wasu bayanan ƙin bayyanar ta su.
Har zuwa yanzu dai yarjejeniyar Sudan ta kudu ba ta aiwatar da tanade-tanaden da ke cikin yarjejeniyar ba, musamman bayan matakin gwamnati na sake ɗage zaɓen ƙasar da aka tsara yi a watan da muke ciki na Disamba.
Wasu bayanai sun ce Sudan ta sanya watan Disamban shekarar 2026 ne don gudanar da zaɓen matakin da tuni ya tunzura ɓangaren ƴan tawaye.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI