A wannan haduwa ta Luanda,bangarorin biyu za su nemi mafita a wannan rikici da suke zargin junan su a bangaren tadda zaune tsaye,lamarin da ya tilastawa mazauna wadanan yankuna tserewa ba tare da shiri ba.
Wasu majiyoyi na bayyana ta yada bangarorin biyu ke aiki tukuru na ganin an samo bakin wannan zare.
Ana kyautata zaton yan lokuta bayan wannan haduwa za a cimma batun janyewar sojojin da kuma kawar da kungiyar yan tawayen M23 masu dauke da makamai.
Dakarun M23 © AFPWani masani a yankin ya kasance cikin shakku game da bayanan da manema labarai suka wallafa.
A hukumance, babu daya daga cikin kasashen da ya tabbatar da cewa za a tattauna batuttuwan da suka jibanci ficewar su daga wasu yankuna duk da yake zance ne na sirri.
Wasu daga cikin mutanen da yakin DRCongo ya tilastawa tserewa daga gidajensu © Hugh Kinsella Cunningham / Hugh Kinsella Cunningham Winner of the 2024 Humanitarian Visa d’or Award - ICRCWasu rahotanni na bayyana cewa , wata majiya ta Congo ta yarda cewa jami'an leken asiri suna goyon bayan wannan tattaunawa kuma manufar Kinshasa ta kasance har yanzu janye sojojin daga Kigali. Ba a bayyana lokacin da za a kamala wannan tattaunawa ba ta Luanda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI