An kawar da yunkurin kashe Shugaban Kasar Madagaska

An kawar da yunkurin kashe Shugaban Kasar Madagaska

A Madagaska an kawar da yunkurin aikata kisan gilla ga Shugaban Kasar Andry Rajoelina.

An kama wadanda aka zargi da yunkurin da suka hada da 'yan kasar kasashen waje.

Game da batun, Babban Mai Gabatar da Kara Berthine Razafiarivony ya sanar da cewa,

"Dalilan da ke hannunmu na nuni da wadannan mutane sun yi shirin kashe Shugaban Kasa da wasu manyan mutane."

Sanarwar ta ce, ana ci gaba da gudanar da bincike.

A shekarar 2019 Rajoelina ya har mulkin Madagaska bayan wani zazzafan zabe.


News Source:   ()