Ƴan kasuwar Kantamanto da ke Ghana sun tafka asarar gaske sanadiyar gobara

Ƴan kasuwar Kantamanto da ke Ghana sun tafka asarar gaske sanadiyar gobara

Hukumar kwana-kwana ta ƙasar ta ce gobarar ta cinye kayayyakin miliyoyin cedi, a kasuwar da ke zama babbar kasuwar sai da kayan tufafi a ƙasar.

Kakakin hukumar kashe gobara ta ƙasar Alex King Nartey, ya ce ba a samu asarar rai ba a sanadiyar gobarar, sai dai an tafka ta dukiya.

Ba a samu asarar rayuka ba, amma anyi da tarin dukiya. Sakamakon binciken farko ya nuna cewa matsalar wutar lantarki ce ta haddasa gobarar, duk da cewa ba mu kammala bincike ba.

Ya ce a yau Juma'a ne suke saran kamma kashe dukkkanin ɓurɓushin gobarar da ta yi saura a kasuwar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)