A watan da ya gabata an kashe 'yan bindiga 80 a arewa maso-yammacin Najeriya sakamakon farmakan da jami'an tsaro suka kai.
Mukaddashin Kakakin Ma'aikatar Tsaro ta Najeriya Bernard Onyeuko ya ce a watan da ya gabata an kai farmakai kan 'yan bindiga a jihohin Zamfara, Katsina da SOkoto.
Onyeuko ya ce an kashe 'yan bindiga 80 sakamakon farmakan inda aka jikkata wasu da dama da suka gudu dauke da raunuka a jikkunansu.
Kakakin ya kuma kara da cewar an kama wasu 'yan bindiga 47, kuma an kwace shanu kusan dubu daya da bindigu 23 daga wajen su.